Colossians 3

Umarnai don Zaman Tsarki

1Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. 2Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. 3Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. 4Saʼad da Kiristi, wanda shi ne ranku,
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da ranmu
ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka.

5Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo shaʼawa a zukatanku: fasikanci, ƙazanta, shaʼawa, muguwar shaʼawa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. 6Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na farko farko suna da zuwa a kan waɗanda suke rashin biyayya
7Dā kun yi waɗannan abubuwa, saʼad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. 8Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. 9Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa. 10Yanzu kowannenku ya zama sabon mutum wanda ake ci gaba da sabuntawa yayinda kuke ƙara sani game da Kiristi wanda ya halicce wannan sabon mutum a cikinku. 11A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai Baʼalʼumme ne ko Bayahude, mai kaciya ne ko marar kaciya, bare, baƙauye, bawa ne ko ʼyantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.

12Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawaliʼu da sauƙinkai da jimrewa. 13Ku rika yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

15Ku bar salamar Kiristi ta yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17Kuma komene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

Umarnai don Iyalan Masu Bi

18Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.

19Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

20ʼYaʼya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.

21Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.

22Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji. 23Komene ne kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. 25Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.

Copyright information for HauSRK